Select a date and time slot to book an Appointment
Date Of Appointment
Shugaba Tinubu Ya Ce An Kashe ‘Yan Ta’adda Sama da 13,000 Cikin Shekara Ɗaya, Hare-haren Ta’addanci Sun Ragu da Kashi 81%
Shugaban Ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya na samun gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga.
A cikin saƙon da ya gabatar na Ranar Dimokuraɗiyya a yau da safiyar Juma’a, Tinubu ya ce yawan mace-macen da ke da alaƙa da ta’addanci ya ragu da kashi 81 cikin ɗari tun daga shekarar 2015.
Shugaban ƙasar ya kuma ce dakarun tsaro sun kashe sama da ‘yan ta’adda 13,000 a cikin shekara guda da ta gabata, tare da ƙara matsin lamba kan masu aikata laifuka a sassa daban-daban na ƙasar.
Tinubu ya gargaɗi ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da su ajiye makamansu su mika wuya, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaron ƙasa.
We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!
Have a great day!
Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support