by Admin
June 19th 2026.
Wata Rundunar Sojoji Ta Musamman Ta Kai Farmaki A Mafakar ‘Yan Bindiga A Ƙaramar Hukumar Matazu 

Wata rundunar sojoji ta musamman ta kai samame a wasu maboyar ‘yan bindiga, a karamar hukumar Matazu inda ta tarwatsa su tare da rusa sansanoninsu.

An gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna inda ‘yan bindigar ke fakewa. Sojojin sun kutsa cikin dajin inda suka kai farmaki a wuraren da ake zargin suna amfani da su wajen shirya hare-hare da kuma ɓoye makamai da ajiye mutanen da suka kama.

A yayin farmakin, ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin tserewa, amma sojojin sun yi musu kwanton ɓauna, wanda ya tilasta musu watsewa a cikin daji kuma daga bisani suka lalata muhimman wuraren buya da kayan aiki da suke amfani da su.

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa wannan farmaki wani ɓangare ne na ci gaba da aikin murƙushe ayyukan ta’addanci a yankin, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a al’ummomin da abin ya shafa.

An kuma shawarci mazauna yankunan da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen kawar da matsalar rashin tsaro a ƙasar.

_katsina post
Search Website

Search

Explore

Tags

Subscribe

Newsletter

WhatsApp Google Map

Safety and Abuse Reporting

Thanks for being awesome!

We appreciate you contacting us. Our support will get back in touch with you soon!

Have a great day!

Are you sure you want to report abuse against this website?

Please note that your query will be processed only if we find it relevant. Rest all requests will be ignored. If you need help with the website, please login to your dashboard and connect to support